30 Satumba 2021 - 13:17
Jagora Ya Nada Peyman Jebelli A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gidan Rediyo Da Talabijin Na Iran

A cikin sanarwar da aka fitar yau Laraba, Ayatollah Imam Khamenei jagoran juyin musulunci na Iran, ya godewa shugaban IRIB mai barin gado Abdul ali Ali-Asgari saboda "kwazonsa" tare da fatan samun nasara ga sabon shugaban hukumar Jebelli a sabon mukaminsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ayatollah Imam Khamenei ya fada a cikin sakon da ya aike wa Jebelli, "Na nada shi da aka yi a matsayin shugaban wannan hukuma na tsawon wa’adin shekaru biyar," ya ce

"Kafofin watsa labarai na kasa wata jami'a ce ta habaka matakin wayar da kan jama'a da ilmi, kuma dandali ne mai fa'ida a idanun kowa.

Akwai abubuwa guda 4 da Jagoran ya zayyana da sabon shugaban zai fi mayar da hankali akai a tsawon shugabancin nasa, su ne Al'adu, karfafa ruhi, juyin juya hali, yada salon rayuwar iraniyawa ta Musulunci , da habaka hadin kan kasa, suna daga cikin manyan abubuwan da yakamata a cimma ta hanyar ingantattun shirye-shirye masu nagarta" inji Imam Khamenei.